MAGANIN GYRAN GASHIN KAI NA MATA
MAGANIN GYRAN GASHIN KAI NA MATA
HABBATUS-SAUDA kashi na Biyar
HABBATUS-SAUDA ko muce HABBATUL-BARAKA duka sunayenta ne, takasance kwaya ce wacce take da albarka, tana maganin kowani irin cuta da yardan ALLAH.
Ana amfani da HABBATUS-SAUDA wajen gyran gashin kai na mata, kamar:
1. Kara Bakin gashi
2. Kara Tsawo gashi
3. Da Laushin gashi
4. Kara Karfin gashi
5. Hana karyewar gashi ko Zuba
*Yadda ake sarrafa wannan maganin asamu:*
1. Man HABBATUS-SAUDA cokali biyar
2. Man ZAITUN kofi days
3. TAFARNUWA kwaya 7 ( adakashi yayi laushi)
Bayan ansamu wadannan abubuwan sai asamo kofi ko wani abu mai kama da kofi azuba man ZAITUN akawo man HABBATUS-SAUDA azuba akawo TAFARNUWA da aka daka azu sai a gaurayasu su cakudu sosai.
Bayan an cakudasu sosai sai asamu woje Mai dubu aboyeshi yadda haske be zai haska shiba har tsawon kwana 40 ko 45.
Amma bayan kowani awa 40 aringa dauko shi ana gauraya shi don maganin yahadu kar yadaskare, zaaga yana sanja Kala.
Bayan maganin yakai wannan kwanakin sai mace tadauko shi nafarko tawanke kanta yafita sosai, na biyu tabar kannata yabushe sosai, na uku sai tadau maganin tashafa a gashin kanta baki daya tacakuda kannata sosai.
Mace zata ringa yin haka sau biyu asati har tsawon wata uku zuwa hudu zatayi mamaki da iznin ALLAH.
Tunanatarwa:
Idan mace zata hada maganin mai yawa sai tasa man HABBATUS-SAUDA misalin kashi daya cikin kashi uku na man ZAITUN.
Misali idan tasamu man ZAITUN kofi uku sai tasamu man HABBATUS-SAUDA kofi daya, TAFARNUWA ma sai tasamu kamar kwaya 12.
Muna godiya da ziyartar wannan shafin, Magani cikin Abinci ataimaka amana like da share don saura su amfana.
Comments
Post a Comment