HABBATUS-SAUDA (kashi na uku)


HABBATUS-SAUDA kwaya ce mai albarka wacce ba'a qayyade iya maganin da takeyi ba, ita HABBATUS-SAUDA tana maganin kowani irin cuta, sai dai tanada hanyoyi daban-daban wajen sarrafata don yin magani.



Yadda ake maganin AMOSANI da HABBATUS-SAUDA


Ita dai cutar AMOSANI cuta ce wacce malaman kiwon lafiya sukace tana cikin jinin mutum, wanda take hana jinin mutum gudana yadda yadace, takan sa jinin mutum yazama ruwa-ruwa sai taje tataru acikin gefen kan mutum.



Alamomin da suke nuna cewa mutum nada ciwon AMOSANI gasu kamar haka:



1. Mutum zai ringa jin idonsa akwai alamar 'kasa ko tsakuwa


2. Mutum zai rufe idonsa yaringa qaiqayawa kamar 'kasa tashiga ciki amma ba abinda yashiga ciki



3. Mutum zai ji yana yawan jin bacci kuma in yakwanta zaiyi baccin



4. Mutum zai ringa jin kasala



5. Idan mutum yafita a titi yana tafiya, sai yasa hannu yana kare idanun sa, bai son rana ta haska idon nasa, idan yabari rana ta haska idonsa zaiji zafi



6. Mutum zaiga idan yashiga rana idanunsa zasuna yin ja



Ga yadda za'a sarrafa HABBATUS-SAUDA don yin maganin AMOSANI asamu:


1. Garin HABBATUS-SAUDA cokali 7


2. Garin ZAITUN cokali 15


3. Man ZOGALE ko man TAFARNUWA ko LALLE


Sai mutum yahadasu waje daya, yashafasu akansa, sai yasamu leda yadaure kannasa dashi, zuwa kimanin minti 20 zuwa 25. Kar yabari yawuce wannan lokacin don zai iya masa illa agashin kanshi.


Mutum zai ringa yin haka sau biyu asati zuwa sawon wata data, Insha ALLAH za'a rabu da ciwon.



Muna godiya da ziyartar wannan shafi, ataimaka amana like da share don saura su amfana.

Comments

Popular posts from this blog

MAGANIN SANYI NA MATA (toilet infection) kashi na daya