HABBATUS-SAUDA (Kashi na daya)

HABBATUS-SAUDA wata kwaya ce wacce take da albarka, wacce ANNABI MUHAMMAD S.A.W. Ya ambace ta, Imamul Bukhari yafitar da hadisi acikin littafi mai suna KITABUL-TIB yasama babin suna, BABUN HABBATUS-SAUDA.


Ita wannan kwaya ana kiranta da sunaye kamar haka:

HABBATUS-SAUDA

HABBATUL-BARAKA

SAUDA'UL-KAMUN

KAMUNAL-ASWAD


Akwai Hadisai guda biyu, gameda wannan kwaya mai labarka (HABBATUL-BARAKA).


(1) An ruwaito diga NANA-AISHA ALLAH yakara mata yarda, tace naji MANZON ALLAH S.A.W. yace " acikin wannan HABBATUS-SAUDA tana maganin dukkan cututtuka sai dai cutar SAM ". Sai nace ya RASULULLAH menene SAM? Sai yace min MUTUWA.


(2) An ruwaito diga Abu-Huraira yace naji MANZON ALLAH S.A.W. Yace " Acikin HABBATUS-SAUDA maganine ta kowani irin cuta sai dai SAM (MUTUWA) ".


Mungode da samun lokacin wajen ziyartar wannan sahafi, ataimaka ayi share don sauran yan uwa su amfana, kuma Kai/ke za'a samu lada.








Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MAGANIN SANYI NA MATA (toilet infection) kashi na daya